Kotun ECOWAS ta umarci Najeriya ta biya Dasuki diyyar N15m

A watan Nuwambar bara ne aka sake kama Sambo Dasuki bayan kotu ta bayar da belinsa
Kotun kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta umarci Najeriya ta biya tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, diyyar naira miliyan 15, bisa tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Kotun wadda ke zamanta a Abuja, babban birnin Najeriyar ta ce a saki shi domin ci gaba da tsare shi da hukumomin kasar ke yi ya keta hakkinsa na dan adam.
Mai shari'a Friday Nwoke da ya sanar da hukuncin kotun a ranar Talata ya ce, tun farko ba a bi ka'ida ba wajen kama Mista Dasuki, sabonda an yi hakan ne babu umarnin 'yan sanda.
Kuma hakan ya sabawa sashe 28 na dokar 'yan sandan Najeriya.
Hukumar tsaron cikin gida ta SSS ce ta sake kama Sambo Dasuki bayan kotu ta bayar da belinsa a watan Nuwambar bara.
Mista Nwoke ya ce takardar umarnin da aka gabatar wa kotun babu sa hannun wanda ya ba da umarni saboda haka shi yasa kotun ba ta yarda cewa sahihi ba ne.
Mista Dasuki dai na fuskantar shari'u daban-daban bisa zarginsa da yin sama da fadi da makudan kudade da aka ware don sayen makamai na yaki da kungiyar Boko Haram a kasar.
Mista Dasuki ya musanta dukkan zarge-zargen yana mai cewa siyasa ce kawai.
Ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami, ya shaida wa BBC cewa gwamnati za ta yi nazari kan hukuncin da zarar ta same shi a hukumance.