An kona wani bangare na kamfanin Dangote a Ethiopia

Motocin kamfanin siminiti na Dangote da aka kona a Ethiopia

Asalin hoton, ZeHabesha.com

Bayanan hoto,

Aliko Dangote shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka

Masu zanga-zanga a kasar Habasha sun kona motoci da wasu kayan aiki a kamfanin siminti na Alhaji Aliko Dangote da ke yankin Oromia .

Masu boren dai na nuna rashin amincewa ne kan kisan akalla mutane 55 a wani turmutsitsin da aka yi a wajen wani bikin addinin da aka yi a ranar Lahadin da ta wuce.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Wasu rahotanni na cewa an kona wani caji ofis tare da sakin wasu fursunoni a lokacin zanga-zangar a yankin Bule Hora.

Masu fafutuka sun ce dakarun tsaron kasar sun bude wuta kan masu bikin bayan sun yi ta wakar bukatar neman 'yancin siyasa.

Abin da gwamnatin ta musanta.

Mista Dangote shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka kuma yana da kamfanoni da masana'antu a kasashe da dama a fadin nahiyar.