Nigeria: Za a sayar da wasu daga jiragen shugaban kasa

An tallata wasu jiragen shugaban Nigeria

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto,

Za a sayar da jirage biyu ne daga cikin goma na shugaban kasa

Gwamnatin Nageriya ta tallata jirage biyu dake cikin rukunin jirage goma na fadar shugaban kasa.

Gwamnatin tayi bayani dalla-dalla a wata sanarwa da aka buga a wasu jaridun kasar kan yanayin jiragen da hotunan ciki da wajensu da kuma ingancinsu.

Sanarwar ta ce ana so a siyar da jiragen biyu kirar Falcon 7X da kuma Hwker 4000 da zarar an samu mai saye.

Kowanne daga cikin jiragen mutune tara yake dauka.

Tun ba yau ba ne 'yan Najeriya da dama suke cewa, kukan karancin kudi da gwamnati ke yi an bar jaki ne ana dukan taiki, saboda yawan jiragen dake fadar shugaban kasa da kuma makuden kudaden da ake kashewa wajen kula da su.

Wadannan jirage dai biyu ne daga cikin goma dake cikin jerin jiragen da ke fadar shugaban Najeriya.

Cikin watan Satumba ne dai mai baiwa shugaban Najeriyar shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya bayyana ne cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tana da shirin rage yawan jiragen dake fadar shugaban kasa.