Nigeria: An yi garkuwa da tsohuwar ministar muhalli

An sace ta tare da mijinta

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Har yanzu ba a san wadanda suka sace Laurencia Laraba Malam

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeria ta ce an sace wata tsohuwar minista da mijinta.

'Yan sandan sun ce an sace tsohuwar ministar ta Muhalli Laurencia Laraba Malam, da mijinta Mr Pious Malam a kan hanyar Abuja babban birnin kasar zuwa Kaduna.

Kakakin rundunar 'yan sandan ASP Aliyu Usman ya ce an sace mutanen tsakanin Bwari da Jere.

Yace mutane shida ne suka tare hanya suka sace su.

"Muna kyautata zaton an yi garkuwa da su ne" inji ASP Aliyu.

Rundunar 'yan sandan tace har yanzu ba ta san inda aka tafi da tsohuwar ministar da mijin na ta ba.

Ana ci gaba da yin garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna duk kuwa da wata runduna ta musamman da aka kafa aka kuma jibge jami'an tsaro da dama a hanyar.

Ko a watan jiya dai sai da aka sa ce wani dan majalisar jahar Kaduna, sannan kuma aka sace wani kusa a jamiyyar APC ta jahar a wannan hanya.

Hukumomi dai na cewa suna iya kokarin su wajen magance matsalar.