Guguwa ta yi mummunan ta'adi a Haiti

Asalin hoton, Reuters
Guguwar ta yi mummunan ta'adi
Mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Mathew mai gudun kilomita dari biyu da ashirin a cikin sa'a guda ta yi ta'adi a Haiti .
Har yanzu ba a san ko mutane nawa ne suka mutu ba.
Guguwar ta lalata amfanin gona da kuma gidajen da ke bakin teku a kudancin kasar.
Tun da farko rahotanni sun ce guguwar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Haiti da kuma wasu hudu a makwabciyar ta, to sai dai daga baya hukumomi sun ce ba a san yawan mutanen da suka mutu ba.
Jami'in majalisar dinkin duniya a Haiti Mourad Wahba ya ce ana bukatar agajin gaggawa a kasar.
Guguwar dai ita ce mafi muni tun bayan mummunar girgizar kasar da akayi shekaru shida da suka gabata.
Yanzu haka dai guguwar ta Mathew ta tasamma Cuba.