Mai yiwuwa Antonio Guterres ya zama Sakatare-Janar na MDD

Antonio Guterres, tsohon firai ministan Portugal

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mista Guterres ya jagoranci hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta MDD

Tsohon firai ministan Portugal, Antonio Guterres, na daf da zama sabon Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar Laraba ne jakadan kasar Rasha a Majalisar, Vitaly Churkin, ya sanar da cewa Mista Guterres, mai shekara 66 da haihuwa, aka fi so.

A ranar Alhamis ne za a kada kuri'a a Kwamitin Sulhu domin tabbatar da dan takarar da aka zaba.

Mista Guterres, wanda ya jagoranci hukamar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya har tsawon shekara 10, zai maye gurbin Ban Ki-moon a shekara mai zuwa.

Mambobin kwamitin sulhun 15 sun kada kuri'unsu a boye ga masu takarar su 10 a ranar Laraba, kuma babu wanda bai amince da Mista Guterres ba.