Nigeria: An sako tsohuwar ministar da aka yi garkuwa da ita

Tsohuwar ministar muhalli Laurencia Laraba Malam

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Tsohuwar ministar muhalli Laurencia Laraba Malam

Rahotanni daga jihar Kaduna a arewacin Nigeria na cewa an sako tshowuhar minsitar muhallin kasar da mjinta, da wasu suka yi garkuwa da su a wannan makon, yayin da suke komawa Kaduna daga Abuja.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna ASP Aliyu Usman ya shedawa BBC cewa an sako mutanen ne a ranar Larabar nan, kuma suna cikin koshin lafiya.

A cikin wannan satin ne dai wasu 'yan bindiga suka tsare tsohuwar ministar Lauracier Malam da Mijinta Pious Malam a tsakanin Bwari da Jere a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sannan suka tafi da su domin yin garkuwa da su.

To sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta Kaduna ba ta yi karin bayani kan ko an biya kudin na fansa ba.

Ana ci gaba da yin garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna duk kuwa da wata runduna ta musamman da aka kafa aka kuma jibge jami'an tsaro da dama a hanyar, domin yaki da masu satar mutanen

Ko a watan jiya dai sai da aka sa ce wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna, sannan kuma aka sace wani kusa a jamiyyar APC ta jahar a wannan hanya.

Hukumomi dai na cewa suna iya kokarin su wajen magance matsalar.