Niger: 'Dage zaben kananan hukumomi ya sabawa doka'

'Yan hamayya sun ce dage zaben ya sabawa doka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Kawancen jam'iyyun hamayya na FRDDR a jamhuriyar Nijar ya ce matakin dage zaben kananan hukumomi da gwamnatin kasar ta yi babu hannusa a ciki.

Shugaban jam'iyar MDND Kokari, Annabo Suma'ila ya ce sun yi watsi da matakin ne saboda taron da majalisar ta CNDP ta yi ya saba wa doka.

Yace dage zaben ya saba doka, kuma za su yaki gwamnati har sai an koma aiki da doka da oda.

Shugaban kawancen na FRDDR ya ce sun shirya tsaf domin shiga zabukan, don haka abinda suka bukata kawai shi ne a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara tun da farko.