Rashin haihuwa: An gudu ba a tsira ba?

Sakamakon binciken bai ba da mamaki ba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sakamakon binciken bai ba da mamaki ba.

Wani bincike da masana kimiyya suka yi ya gano cewa 'ya'yan da ake haifa ta hanyar magungunan da ke taimakawa wajen iya haihuwa suna gadon cutar rashin haihuwa.

Masanan na Jami'ar Brussels sun gano cewa yaran da ake haifa ta hanyar diban maniyyin namiji sannan a zuba shi kai-tsaye cikin mahaifar mace, wato IVF na iya yin fama da cutar rashin haihuwa idan sun girma.

Masanan sun ce sakamakon binciken bai ba su mamaki ba.

Sun kara da cewa za su tabbatar da wannan bincike ne idan 'ya'yan da aka haifa ta wannan hanya a farkon shekarar 1990 sun yi aure.