An amince a ci gaba da zubar da ciki a Poland

Poland

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An yi zanga-zangar adawa da kudirin dokar

'Yan majalisar dokokin Poland sun yi watsi da wani kudirin doka mai cike da ce-ce-ku-ce, wanda ya so hana mata zubar da ciki dungurungun.

Gwamnati dai ta ce zanga-zangar da aka rika yi ta nuna kin jinin kudirin dokar ta sa ta yi karatun ta-nutsu.

Da ma dai kasar ta Poland tana son hana zubar da cikin dungurungun sai dai idan yin hakan zai jefa mace cikin hatsarin rasa ranta.

'Yan majalisa 352 ne suka amince da dokar yayin da 'yan majalisa 58 suka yi watsi da ita.

'Yan kasar da ke adawa da zubar da ciki ne suka dauki nauyin kudirin dokar tare da goyon bayan cocin katolika ta kasar.