Wanene zai iya gyara Kannywood?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Rahama Sadau

Asalin hoton, FINESSE ENTERTAINMENT

Bayanan hoto,

MOPPAN ta ce rungumar Classiq da Rahama Sadau ta yi ta saba da ka'idojin kungiyar

Kurar da ta taso tun lokacin da fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta fito a bidiyon waka, inda ta rika rungumar mawaki Classiq da kuma ce-ce-ku-cen da korarta daga yin fina-finan suka kawo ta sa masu nazari a kan Kannywood na tambaya: shin wanene zai iya kawo gyara a wannan masana'anta?

Tarihin Kannywood dai cike yake da kalubale musamman yadda al'uma Hausa ke daukar masu yin fina-finan a matsayin mutanen da ke kokarin ruguza al'uma da bata tarbiyya.

Kuma da alama duk da kokarin da wasu daga cikin masu yin fina-finan ke yi na nuna wa al'uma cewa babban burinsu shi ne su ilimantar da al'uma da kuma nishadantar da ita, hakan bai yi wani gagarumin tasiri kan irin kallon hadarin-kajin da ake yi musu ba.

Al'amura da dama sun faru a baya bayan nan da ke nuna cewa har yanzu al'uma ba ta gamsu da kokarin da masu yin fina-finan ke yi na samun karbuwa a cikin al'uma ba.

Babba daga cikin shi ne yunkurin da aka yi na gina alkaryar fina-finai a jihar Kano -- wacce kodayake ta samu goyon bayan hukumomin jihar, amma watsin da Malamai suka yi da ita ya sa dole aka janye daga gina ta.

Malaman dai sun nanata cewa gina alkaryar zai kara zaizaiye tarbiyyar jama'a, kodayake masu ruwa-da-tsaki a Kannywood sun yi ta musanta hakan, suna masu cewa an yi wa shirin gurguwar fahimta.

Asalin hoton, AlI NUHU

Bayanan hoto,

Ali Nuhu na cikin 'yan wasan da suka sauya alkiblar Kannywood

Don haka korar da aka yi wa Rahama Sadau wata alama ce da ke nuna cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da karbuwar fina-finan Kannywood a wajen wani bangare na al'umar Hausa.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Yaushe za a gano bakin-zaren?

Da farko dai dole masu harkar fim din Kannywood su sani cewa kurarsu ta riga ta yi kuka don haka gyra gidansu shi ne babban abin da ya kamata su sanya a gaba, ba fadace-fadace da rashin jituwa tsakaninsu ba.

Kuma kamar yadda daya daga cikinsu, Abdul Amart ke cewa, "Matsalolin da Kannywood ke fama da su da dama za su kare ne idan muka tattauna da juna, maimakon yin gulma da juna".

Gwamnatoci da dama da masu sharhi sun yi ta yunkurin kawo gyara a Kannywood, musamman ganin irin kudin shigar da fannin ke samarwa gwamnati, baya ga dumbin ayyukan yin da yake samarwa mutane.

Hukumar tace fina-finan jihar Kano ta sha daukar matakai na kawo karshen "rashin tarbiyyar" da wasu masu yin fina-finan ke nunawa.

Ko da a farkon wannan shekarar sai da hukumar ta sa aka kama wasu jaruman fina-finan da suka fito da wani fim da, a cewarta, bai cika ka'idojinta ba amma babu wanda ya kara jin abin da ya faru.

Wasu na zargin cewa hukumar na yin hukunci ne kawai a kan mutanen da ba su da uwa a gindin murhu, kodayake ta musanta hakan.

Ita kanta kungiyar masu harkar shirya fina-finan Kannywood, MOPPAN, babu wani tasiri da take yi na kawo dawwamammen gyara a fina-finan na Hausa.

Hasalima, wasu na ganin ba ta shimfida wasu dokoki da ke yi wa 'yan fim din shamaki ba, shi ya sa suke cin karensu babu babbaka.

Masu nazari dai na ganin za a kawo gyara ne kawai a Kannywood idan gwamnati -- wacce ita ce ke da wuka da nama wajen tabbatar da doka -- ta dauki matakin ba-sani-ba-sabo kan duk wanda ya keta doka, sannan ta karrama duk mutumin da ya yi wata bajinta a bainar jama'a.