Yadda matasa ke kokarin zama marubuta

  • Isa Sanusi
  • BBC Hausa, Abuja
Hilltop Arts
Bayanan hoto,

Matasa da dama ne ake yaye wa a Cibiyar Hilltop Arts a kowacce shekara

A kan tsaunin Minna, babban birnin jihar Niger a Najeriya, a kowacce rana matasa daga kowanne bangare na birnin suna taruwa a Hilltop Arts Centre domin koyon wani bangare na adabi, da kuma zane-zane da yadda ake shirya fina-finai.

Ya zuwa yanzu dai wannan cibiya ta yaye matasa da dama da daga bisani suka zama marubuta.

Tun daga watan Janairu har zuwa watan Disamba na kowacce shekara a karshen kowanne wata cibiyar tana kaddamar da marubuci ko marubuciya da ake ganin sun kama hanyar gogewa.

Yayin kaddamarwar maburucin zai bayyana a gaban jama'a inda zai hau dandali ya karanta abin da ya rubuta.

Daga nan kuma sai a bude fili ga masu tambayoyi da kuma masu bada shawara.

Bayan wannan sai kuma a duba irin hanyoyin da za a bi domin wallafa abin da marubucin ya rubuta.

Malam Baba Muhammed Dzukogi shi ne ya kafa wannan cibiya kuma ya ce, "na lura cewa, matasa suna da abin fadi, kuma kamata yayi al'umma ta maida hankali wajen dora rayuwarsu akan turba mai kyau tun suna kanana.

Yawancin iyaye ba su damu da abin da 'ya 'yansu suke yi ba, dan haka wasu suke shiga wani hali. Na dauki nauyin gudanar da wannan aiki ne domin gobe ta yi kyau a wannan al'umma."

Bayanan hoto,

Dzukogi shi ne ya kafa wannan cibiya ta Hillltop Arts Centre

Baba Dzukogi ya ce, wasu iyayen suna kawo 'ya 'yansu da kansu domin suna son su ko yi rubuce-rubuce.

Matasa wadanda yawancinsu 'yan sakandire ne su ne suke halartar wannan cibiya inda ake gudanar da aji na koyar da rubuta kagaggun labarai, da rubutattun wakoki, da zane-zane, da waka da kuma yadda ake shirya fina-finai.

Halima Aliyu ta shiga wannan cibiya tun tana matakin farko na karatun sakandire, amma yanzu ta rubuta litattafai da dama, kuma ta dawo wannan cibiya inda take koyar da matasa dabarun rubutun adabi.

"Yawancin matasa ba sa fadawa kowa abin da yake damunsu, ko abin da bai musu dadi ba a rayuwa, amma rubutu wata hanya ce da mutum zai bayyana abin da yake cikin zuciyarsa, da kuma yadda yake kallon al'umma."

Halima tana gudanar da ajinta wanda yawancin dalibanta mata ne.

Kuma ta ce, ya kamata a karfafa wa mata gwiwa sosai a al'umma domin su ne suke bada tarbiyya.

Bayanan hoto,

Halima Aliyu ta shiga wannan cibiya tun tana matakin farko na karatun sakandire

Akwai dai dakin karatu cike da litattafai a wannan cibiya, haka kuma akwai a fagen da ake zane-zane.

A ina ake samun kudin gudanarwa?

A cewar Baba Dzukogi, suna neman taimako daga masu karfi, da kuma sayar da irin wasu daga cikin zane-zanen da matasan suka yi.

Duk da yadda hanyoyin sadarwa na zamani suke kara yin tasiri, wannan cibiya tana samun dimbin matasa wadanda su burinsu shi ne su dau littafi su karanta.

Success M Yusuf matashiya ce da ta rubuta wata waka mai suna 'Tears' wato hawaye, inda a ciki ta tabo batutuwa da dama kamar matsalar tsaro a Najeriya da kuma batun rikicin Boko Haram, da sace 'yan matan Chibok da matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki.

Ta ce, "Wannan waka na yi ta ne domin bayyana damuwata akan halin da Nigeria take ciki da kuma bukatar na gaba da mu su dau mataki domin gobe ta yi kyau."

Bayanan hoto,

Yawancin daliban Halima Aliyu mata ne

Bayanan hoto,

Matasa daga kowanne bangare na birnin suna taruwa a Hilltop Arts Centre

Wannan cibiya wata alama ce cewa, duk da tsadar litattafai da kuma koma-bayan masu karanta su, akwai matasan da suka maida hankali wajen ganin sun habaka basirarsu.

Daga lokacin da aka kafa wannan cibiya a shekara 2004 zuwa yanzu, an wallafa littafan da matasa da dama suka rubuta bayan sun samu horo a wannan cibiya.

Matasa da dama suna yin rubuce-rubuce akan matsalolinsu, amma wasu suna ma yin rubutun akan matsalolin da suka addabi Najeriya.

Kuma a cewar Baba Dzukogi, wannan alama ce cewa, manyan gobe za su taka rawa wajen kaucewa irin kura-kuran da suka jefa Najeriya cikin halin da take ciki yanzu haka.