An kashe sojoji sama da 20 a Jamhuriyar Nijar

Sojojin kasar sun bazama domin neman maharan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kashe sojojin Nijar a wani hari

Rahotanni daga yankin Tasara a jahar Tawa da ke arewacin Jamhuriyar Nijar sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe sojoji 22 a wani mummunan hari da aka kai musu.

Firayi ministan kasar Malam Biriji Rafini ya tabbatar da kai harin ga sojojin da ke tsare wani sansanin 'yan gudun hijira a garin Tazali a gundumar Tasara.

Yace an yi wa sojojin ba-zata ne, inda aka kashe 22.

Fara ministan ya ce mutuwar sojojin babbar asara ce ga jamhuriyar Nijar.

Wasu bayanai sun ce an kai akalla sojoji biyu asibiti domin yi musu maganin raunin da suka samu.

Sansanin dai wanda ya ke garin Tazali na 'yan gudun hijira ne daga arewacin Mali.

Hukumar kula da 'yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wacce ke da ma'aikata a sansanin ta ce wasu 'yan bindiga ne suka afkawa sansanin ranar Alhamis a motoci masu yawa.

Bayan harin da suka kai dai sun tsere ta kan iyakar Nijar da Mali.

Tuni dai sojojin Nijar suka bazama domin farautar maharan.

Jamhuriyar ta Nijar dai ta fara fuskantar hare-hare tun bayan barkewar rikici a kasar Mali mai makwabtaka.

A baya ma dai an taba kai wani hari a yakin Walam da ke jihar Tillaberi inda aka kashe sojojin Nijar da dama.

Har yanzu dai ba a san ko su waye suka kai harin ba, amma a baya an zargi 'yan tawayen Mujao da kai irin wadannan hare-hare a jamhuriyar ta Nijar.