Nigeria: jam'iyyar PDP za ta sasanta rikicin yayanta

PDP ta jima cikin rikici

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a yi shulhu a jam'iyyar PDP

A Najeriya, babbar jam`iyyar adawar kasar PDP, ta yi wani sabon yunkuri don magance rikicin shugabancin da ya dabaibaye ta.

Yanzu dai bangaren da ke karkashin Senata Ahmed Makarfi da na Senata Ali Madu Sherif duka sun amince da kafa wani kwamitin hadin-gwiwa da zai lalubo hanyar sulhu mai dorewa.

To sai dai wasu masu sharhi na ganin da wuya a iya sasanta rikicin na PDP, sabo da jam'iyyar ba ta daukar matakan da suka kamata da kowane bangare zai gamsu cewa an yi masa adalci.

Wani masanin kimiyyar siyasa Farfesa Jibrin Ibrahim na ganin hanyar da ya kamata PDP ta bi shi ne zaben raba gardama a duk lokacin da ake takaddama.

"To su ba sa iya zabe in ba an yi coge ba" In ji Farfesa Ibrahim.

Hanya ta biyu kuma a cewar Farfesa ita ce a garzaya gaban kotu.

"Duka hanyoyin biyu ba sa aiki".

Jam`iyyar dai ta fada rikicin shugabanci ne tun bayan kayin da ta sha a zaben shugaban kasa.