Ga abin da za ka yi idan aka kore ka daga aiki

Sree Sreenivasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hulda da jama'a a dandalin sada zumunta na da ranarta

Bayan da Sree Sreenivasan ya rasa aikinsa na shugaban sashen fasahar sadarwa na gidan adana kayan tarihi na New York Metropolitan, ya dauki wani matakin da ba kowa ne zai dauki irinsa ba, wato ya yada labarin ga dubban abokansa da ke Facebook.

Sreenivasan ya shaida wa duniya dalilin korarsa ("Tsuke bakin aljihu"), ya kuma gayyaci abokansa zuwa shan gahawa ko kuma su je shan iska a wurin shakatawa na Central Park (Saboda yanzu yana da lokaci), sannan kuma ya bukaci mutane su cike wani fom a shafin matambayi baya bata na Google, don taimaka masa da shawarwarin me yakamata ya yi nan gaba.

Wannan sanarwar ta Sreenivasan ta biya bukata, domin fiye da mutane 1,200 ne suka latsa 'so' a kasan bayanin nasa, yayin da mutane 1,300 kuma suka ba shi shawarwari kan aikin da zai yi.

Daga cikinsu ma har akwai wadanda suka yi masa tayin ba shi aiki.

Bayan watanni kadan kuwa ya sami aikin shugabancin sashen fasahar sadarwa na birnin New York baki daya.

A cewar Sreenivasan, ya samu mukamin ne "Saboda mahukuntan New York sun karanta a Facebook cewa ina neman aiki."

Maraba da shekarar 2016 da kuma sabon salon neman aiki da ta zo da shi.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Hakika Sreenivasan ya amfana da cewa dama yana da dubban abokai a Facebook kuma kwararre ne wurin amfani da dandalin sada zumunta.

Mu kuma fa? Shin wannan matakin zai taimaki masu abokai 500 sabanin Sreenivasan da ke da 5,000?

Amsar anan ita ce "e", in ji Sreenivasan.

Amma ka yi yadda zai dace da kai. "Ba lallai ba ne sai ka yada wa duniya. Kana iya rubuta wa 15 daga cikin makusantan abokanka ka shaida musu halin da ka shiga. Ba sai ka yayata wa miliyoyin mutane ba. Bukatar dai ka sanar da wadanda za su iya taimakonka."

Ka da kuma kurum ka ce musu kana neman taimako. "Yi bayani dalla-dalla game da abubuwan da ka iya da kuma irin aikin da ka ke nema, saboda ko makusantanka ba lallai ba ne su san takamaiman abin da ka ke yi ba, ko kuma abin da za ka iya yi ba," a cewarsa.

Akwai darasi

Ka da ka jira sai ka na cikin bukata sannan ka fara neman mutane.

"Yi hulda da jama'a lokacin da baka bukatarsu. Kulla alaka a lokacin da baka cikin wata matsala," in ji Sreenivasan.

Abin babu wuya; ka rika aika musu sakon text ko ka kira a gaisa ko kuma ka rika yin martani idan sun wallafa wani abu a Facebook ko kuma akalla ka latsa 'so'.

Ya ce: "Shi ke nan abin da za ka rinka yi, to da ka shiga matsala dama kana da abokan hulda."

Wannan zai taimaka maka samun tallafi daga mutanen da kake da alaka ta nesa da su, wadanda su ne zasu fi iya samo maka aiki, a cewar malama a makarantar nazarin kasuwanci ta nahiyar Turai da ke birnin London (ESCP), Claudia Jonczyk.

Mutane su kan yi kuskuren zaton cewa mutanen da suka fi kusanci da su su ne za su fi taimakonsu wurin samun aiki.

Amma wandannan makusantan "yawanci suna da irn matsayi da tasirin da kai ma ka ke da su ne," in ji Jonczyk.

Maimakon haka, mutanen da ku ke da alaka ta nesa ne suke da matsayin da za su iya sanin wani wanda shi kuma ya san wanin da zai iya taimaka maka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hannu daya baya daukar jinka

Magana zarar bunu

Lokacin da ka ke tunanin abin da zaka wallafa a dandalin sada zumunta, yana da matukar muhimmanci "ka tuna cewa a wannan zamanin na fasaha, duk abin da ka yi ba ka iya kankare shi," in ji shugaban kamfanin daukar manyan ma'aikata na Webber Kerr Associates dake Florida a Amurka, Adam Lloyd.

Don haka ka yi taka-tsantsan da abin da zaka wallafa a dandalin sada zumunta. Idan sakon naka bai dace ba, kar ka wallafa shi. Kullum ka tambayi kanka," in ji Lloyd: "Me zan karu da shi idan na wallafa, kuma mai zan rasa?"

Yayin da rubuta kalmomin cin mutunci game da tsohon kamfanin da ka yi wa aiki zai faranta maka rai a lokacin, wallafa irin wadannan bayanan ba daidai ba ne a dandalin sada zumunta, ko da kuwa manufarka ita ce ka gargadi masu neman aiki a wurin da su yi hattara da kamfanin.

Za ka iya jan hankalin mutane da dama, amma "wadanda za su iya daukarka aiki a gaba za su yi maka mummunar fahimta, tare da daukar cewa su ma in ka bar su za ka tozartasu," a cewar Lloyd.

Lloyd ya ba da shawarar dakatawa kafin ka wallafa wani abu. "Idan ka yanke hukuncin wallafa wani abu, to ina baka shawarar ka jinkirta, kar ka wallafa cikin fushi, kar ka soki kowa, kar ka tona asirin kamfani, kawai ka bayyana gaskiya zallanta." Bugu da kari ka yi la'akari da dandalin da ka ke wallafawar. Ya ce; "Abin da za ka wallafa a Facebook ba shi ya dace ka wallafa a LinkedIn ba."

Akwai kuma bambanci na al'adar kasar da ka ke, in ji Jonczyk. "Kora daga aiki abin kunya ne a Faransa da Jamus, sabanin kasashen da aka saba sallamar ma'aikata ba don sun yi laifi ba." Don haka ya kamata ka yi la'akari da wannan kafin ka wallafa bayanin.

Irin aikin da ka ke nema ma zai iya taimaka maka wurin yanke hukuncin yadawa ko a'a, in ji shugabar kamfanin ChameleonResumes.com dake birnin New York, Lisa Rangel.

Ta ce "Idan kwarewa a ta'ammali da dandalin sada zumunta na daga cikin abubuwan da ake bukata a aikin, to ka yi dabara ba karama ba idan ka wallafa neman, amma idan aiki ne da ke bukatar sirri, yayatawa ba dabara ce mai kyau ba."

Ko ma dai wani irin aiki ka ke nema, ka tabbatar ba ka keta haddin tsohon kamfanin da ka yi aiki ba, ko kuma shugaban da ka yi aiki a karkashinsa, in ji Rangel.

Ya ce; "Babu inda hakan ya taba yin amfani. Abin da ya kamata shi ne ka nuna cewa barinka wancan wurin wata dama ce ta koyon sababbin abubuwa."