Gwamnatin Nigeria ta janye karar da ta shigar kan Saraki

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Alhamis ne gwamnati ta mika bukatar janye karar a gaban wata babbar kotun birnin Abuja
Gwamnatin Najeriya ta janye zargin da take yi wa Shugaban Majalisar Dattawan kasar, Bukola Saraki da Mataimakinsa Ike Ekweremadu, na hada baki wajen yin dokokin bogi don hawa mulki.
Lauyan da ke wakiltar gwamnati a shari'ar, Barista Aliyu Umar, ya yi gyara a tuhume-tuhumen da ake wa mutanen bayan ya yi nazari kan karar.
Sai dai a sabuwar karar da aka fara sauraronta a ranar Juma'a babu sunayen shugaban majalisar dattawan da kuma mataimakinsa, sai tsohon akawun majalisar Alhaji Salisu Maikasuwa da mataimakinsa Ben Efeturi ne kawai.
Tuni ofishin Mista Saraki ya yi maraba da matakin janye karar a kansu, yana mai cewa dama siyasa ce kawai ta sa aka tuhume shi.
Wasu dai na kallon matakin janye karar da gwamnatin ta yi a kan Saraki da mataimakinsa, wata alama ce da ke nuna cewa ba da gaske take yi ba a ikirarin da take na yaki da cin hanci da tabbatar da doka da oda.
Sabuwar karar dai na zargin Maikasuwa da kuma Efeturi ne da hada baki wajen kirkiro dokoki na jabu ba tare da amincewar majalisar dokokin da ta shude ba,.
Sannan ta tuhume su da niyyar sa 'yan majalisar dattawa na yanzu amfani da su a zaman dokokin majalisar na kwarai da zauren da ya shude ya amince da su.
Haka ma ana zargin sun bayar da bayanan da ba na gaskiya ba da niyyar yi wa jama'ar kasar bad-da-bami.
Kokarin da BBC ta yi na samun karin bayani daga ma'aikatar shari'ar ko daga wajen babban Atoni Janar na kasar bai yi nasara ba.
A ranar 10 ga watan Yunin shekarar 2016 ne gwamnatin Najeriyar ta shigar da karar Mista Saraki da Ike Ekerenmadu, da tsohon akawun majalisar da mataimakinsa a gaban kotu bisa zargin yin dokokin na bogi, zargin da suka sha musanta wa.