Me zai faru idan kwatsam aka daina cin nama a duniya?

Asalin hoton, iStock
Za a rage yawan mutuwa da miliyan bakwai idan an daina cin nama nan da shekarar 2050
Cire nama daga cikin jerin abincinmu zai kawo dimbin ci gaba ga lafiyarmu da kuma muhallinmu - amma zai cutar da miliyoyin mutane.
Mutane na daina cin nama saboda dalilai daban-daban, wadansu don tausayin dabbobi, wasu kuma don samun karin lafiya, wasu kuma suna yi ne saboda kyautata muhalli ta hanyar rage yawan iska mai gurbata yanayi.
Duk musun da maciya nama zasu yi, mutanen da basa cin nama na da gaskiya, domin daina cin nama na da dumbin amfani.
Kuma idan mutane da dama su ka daina, amfanin zai ci gaba da yaduwa a ban kasa.
Sai dai kuma, idan kowa ya daina cin nama, miliyoyi ko ma biliyoyin mutane za su shiga uku.
"A gaskiyar magana duniya ta rabu gida biyu," in ji Andrew Jarvis na cibiyar nazarin noma a kasashe masu zafi, ta Colombia. "A kasashen da suka ci gaba, rashin cin nama zai kawo ingancin lafiya da muhalli, amma a kasashe masu tasowa, rashin cin nama zai haddasa mummunan talauci."
Jarvis da sauran kwararru na cibiyar na hasashen abin da zai faru idan dare daya aka daina cin nama a fadin duniya.
Sauyin yanayi
Sun fara da nazarin sauyin yanayi: Samar da abinci shi ke kawo rubu'i zuwa sulusin iskar da ke gurbata muhalli a fadin duniya, kuma mafi yawan nauyin yafi rataya a wuyan masu kiwon dabbobi.
Duk da haka ba a cika kulawa da lahanin da abincinmu ke yi wa muhalli ba.
Ga misali a kasar Amurka, iyali mai mutune hudu kan samar da iskar da ke gurbata abinci daga naman da suke ci wadda ta zarta ta motoci biyu da suke tukawa - amma kullum motocin ake sa wa ido maimakon tsire a duk lokacin da ake tattauna batun gurbata muhalli.
"Mafi yawan mutane ba sa tunanin tasirin abinci a kan sauyin yanayi," in ji wani kwararre a kan wadatar abinci da ke jami'ar Leeds a Ingila, Tim Benton.
Asalin hoton, iStock
Daina cin nama a fadin duniya zai fi mummunan tasiri a kan kasashe masu tasowa
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of Podcast
Ya ce; "Rage cin nama a yanzu zai taimakawa rayuwar 'ya'yanmu da jikokinmu a nan gaba."
Manazarci a cibiyar bincike kan makomar abinci a makarantar Martin ta jami'ar Oxford, Marco Springmann, na kokarin lissafa ci gaban da za'a samu: shi da abokan aikinsa sun samar da wani jadawalin kwamfuta da ke kididdiga abin da zai faru idan kowa ya daina cin nama nan da shekarar 2050.
Sakamakon ya nuna cewa rashin cin nama zai rage samar da iska mai gurbata yanayi da kaso 60 cikin dari.
Idan kuwa aka daina cin duk abin da ya fito daga jikin dabbobi, adadin iskar zai ragu da kaso 70cikin dari.
Haka kuma, kiwon dabbobi na cin wuri da yawa - abin da ke jawo karuwar iska mai gurbata yanayi tare kuma da rage wadatar shuke-shuke a ban kasa.
Daga cikin kimanin hekta biliyan biyar (wato eka biliyan 12) da ake amfani da su wurin noma da kiwo, dabbobi na cinye kaso 68 cikin dari.
Da gaba dayanmu zamu daina cin nama kwata-kwata da akalla kaso 80 cikin dari na wuraren kiwo za su koma daji, abin da zai taimaka wurin rage sauyin yanayi.
Haka kuma mayar da wuraren kiwo zuwa dazuzzuka zai kara yalwar halittu irinsu bakane wanda aka kore su saboda shanu, da kuma dabbobin farauta irin su kyarkeci wadanda akan kashe su domin kare shanu.
Ragowar kaso 10 cikin dari zuwa 20 cikin dari na filayen kiwo kuma sai a mayar da su gonaki domin samun karin abinci.
Duk da kasar noman ba za ta karu da yawa ba, amma hakan zai cike gibin naman da za'a rasa kasancewar sulusin kasar noman duniya ana amfani da ita domin samar wa dabbobi abinci - ba mutane ba.
Sai dai kuma mayar da makiyaya zuwa dazuzzuka na bukatar kashe kudi. "Ba za ka dauke shanu daga makiyaya ba kawai tsammanin za su koma dazuzzuka kai tsaye," in ji Jarvis.
Kiwo da fawa
Mutanen da ke rayuwa bisa sana'ar samar da nama ma za su bukaci tallafi, domin karkata akalar rayuwarsu zuwa wasu sana'o'in da su ka danganci noma, ko sake samar da dazuzzuka, ko kuma samar da makamashi daga sassan tsirran da a yanzu ake amfani da su wurin ciyar da dabbobi.
Ana kuma iya biyan wasu makiyayan su ci gaba da ajiye dabbobi domin kyautata muhalli. "Yanzu haka ina Scotland inda kiwon raguna ne ya samar da muhallin da muke ciki," in ji wani mai bincike a kan tsarin muhalli a jami'ar Ediburgh, Peter Alexander. "Idan mu ka kwashe ragunan gaba daya, muhallin zai sauya kuma akwai barazanar rage yawaltar halittu."
Idan muka gaza samar da makoma ga makiyaya, ana iya samun rashin aikin yi da kuma rigingimu musamman a kauyukan da suka dogara da kiwo.
Asalin hoton, iStock
Daina sa nama cikin jerin abincinmu zai kawo habakar tattalin arziki
"Ana yanka sama da tumaki da shanu da aladu biliyan uku da rabi, da kuma gomiyar biliyoyin kaji a kowacce shekara a fadin duniya," in ji wani wanda ke bincike kan daidaita tsakanin bukatar abinci da samar da yalwar halittu a jami'ar Cambridge, Ben Phalan. Ya ce; "Daina cin nama zai haddasa mummunar karayar tattalin arziki."
Sai dai fa komai dabarar da za'a yi, ba za'a iya samar da sana'a ga duk wadanda za su bar kiwo ba.
Kusan sulusin kasar duniya ba za ta nomu ba sai dai ayi kiwo kawai.
A baya, wasu sun yi kokarin noma a yankin Sahel na yammacin Afirka, amma babu abin da hakan ya haifar sai kwararar hamada da dimbin asara.
"Idan babu dabbobi, rayuwar mutane ba za ta yiwu ba a wasu sassan duniya," in ji Phalan.
Wadannan sassan sun hada da makiyayan kabilun Mongol da Berber, wadanda zaman gida zai kama su idan aka raba su da dabbobinsu, abin da zai kawo karshen al'adunsu da dabi'unsu.
Kai, wadanda ma ba da dabbobin suka dogara ba sai sun yi asara.
Bukukuwa
Nama na da muhimmanci a tarihi da al'adun al'ummomi da dama.
Kabilu da yawa a fadin duniya kan yi kyautar dabbobi lokacin bukukuwa, bukukuwan kirsimeti sun kafu akan cin nama, sannan kuma wadansu girke-girken da ake yi da nama sun zama abin alfahari ga wasu al'ummomin duniya. "Tasirin da daina cin nama zai yi wa al'adu yana da matukar yawa, abin da ya sa kenan kokarin rage cin sa ma ke haduwa da cikas," in ji Phalan.
Tasirin daina cin nama ga lafiya ma ya bambanta.
Awon kwamfutar da Springmann ke gudanarwa ya nuna cewa da kowa zai daina cin nama nan da shekarar 2050, za'a rage mutuwa da kaso shida cikin dari, saboda raguwar ciwon zuciya, ciwon sukari da kuma cutar kansa.
Daina cin nama zai rage mace-mace miliyan bakwai a fadin duniya, yayin da daina amfani da duk abincin da ake samu daga dabbobi zai rage mutuwar mutane miliyan takwas a duniya.
Haka kuma raguwar mutane masu fama da cututtukan da suka danganci cin nama zai rage kudaden magani, abin da zai sa tattalin arzikin duniya ya karu da kaso biyu zuwa uku cikin dari.
Asalin hoton, iStock
Babu wata dabarar da za a yi da zata cike gurbin wadanda za a raba da hanyar cin abincincu idan an daina cin nama a fadin duniya
Sai dai kuma ba za'a samu wannan amfanin ba sai an maye gurbin naman da abinci mai gina jiki.
Abincin da ake samu daga dabbobi sun fi wadanda ake samu daga tsirrai abubuwa masu gina jiki.
Don haka daina cin nama barazana ce ga fiye da mutane biliyan biyu a fadin duniya wadanda yanzu ma suke fama da karancin abinci.
Rage cin nama
Abin farin cikin shi ne, ba sai duk duniya ta daina cin nama ba ne za'a iya samun wadannan amfanin, amma mafita ita ce rage cin nama.
Wani nazari ya gano cewa bin shawarar hukumar lafiya ta duniya, wurin tsarin cin abinci zai rage iska mai gurbata yanayi da kasar Burtaniya ke samarwa da kaso 17 cikin dari - abin da zai iya raguwa da karin kaso 40 cikin dari inda 'yan kasar zasu rage cin dabbobi da kuma kayan kwalam da makulashe. "Wadannan sauye-sauye ne da ba za su gagara ba, irinsu rage girman yankan nama," in ji Jarvis.
Kawo sauye-sauye a tsarin samar da abinci zai kara mana azama wajen cin abincin da zai kara mana lafiya tare da inganta muhalli, in ji Springmann - irinsu kara farashin nama tare da sauwake farashin kayan marmari da ganyaye a fadin duniya.
Rage al'mubazzaranci ma zai taimaka domin kuwa kasa da rabin abincin da ake samarwa ne ake amfani da shi yadda ya dace.
"Akwai hanyoyin da za'a iya inganta samar da dabbobi tare da karin riba ga makiyaya" in ji Benton.
Sai dai kuma amfani da su ne ke gagara, saboda mahukunta ba sa daukar matakan da za su kawo sauyi.