Mutane 800 sun mutu a Haiti sakamakon mummunar guguwa

Mutane 800 ne suka mutu sakamakon guguwar

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Guguwar ta yi kaca-kaca da garuruwa a Haiti

Mahukunta a Haiti sun ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 800 sakamakon mummunar guguwar da aka yiwa lakabi da Matthew, wadda ta afkawa kasar a ranar Talatar da ta gabata.

Jami'an agaji na majalisar dinkin duniya sun yi gargadin cewa za a dauki kwanaki kafin a farfado daga illar da guguwar ta yi.

Guguwar dai ta afkawa kudu maso yammacin kasar ne, inda ta yi mummunar barna a garin Jeremie.

Carlos Veloso na hukumar samar da abinci ta duniya ya shaidawa BBC cewa, tuni aka fara kai kayan agaji, sai dai kuma barnar da guguwar ta yi a yankin ta sa an kasa shiga yankin saboda rashin hanya, sai dai a shiga ta jirgi mai saukar ungulu ko kuma ta ruwa.

Ya ce har yanzu ba za a iya kaiwa ga wasu kauyuka dake gabar teku ba wanda guguwar ta shafa , sannan kuma akwai fargabar yaduwar cutukan da ake dauka a ruwa.