Ana cece-kuce tsakanin Amurka da Rasha akan zargin satar bayanai

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta zargi Rasha da satar Bayanai
Rasha ta yi watsi da zarge-zargen da gwamnatin Amurka ta yi mata inda ta ce ta na da hannu a satar bayanan sirri da ake yi mata da nufin kawo rudani a gangamin yakin neman zaben shugaban kasar da ake yi.
Mai magana da yawun gwamnatin Rasha ya ce wadannan zarge-zarge soki burutsu ne, in da ya ce suma fa a kowacce rana akan yi kutse a shafin yanar gizon shugaba Putin, amma ba su zargi kowa ba.
Amurkan ta ce kutsen da ake yi cikin wasu komputoci wanda suke mallakar jam'iyyar Democrat ne, manyan jami'an Rasha ne kawai za su bayar da umarnin yin sa.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 22/01/2021, Tsawon lokaci 1,09
Minti Ɗaya Da BBC Na Rana 22/01/2021