An ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a jihar Bauchi

An sace mutanen ne a karamar hukumar Ningi
Bayanan hoto,

An ceto mutane 11 a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a Nijeriya na cewa an kubutar da mutanen nan goma sha daya da suka hada da mata da jarirai wadanda wasu 'yan bindiga suka sace a karamar hukumar Ningi.

A ranar Lahadi da ta gabata ne 'yan bindigar suka sace mutanen a wani hari da suka kai a kauyen Nipchi.

kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ta Bauchi ASP Muhammad Mahmud ya shaida wa BBC cewa baya ga kubutar da mutanen da aka sace, jami'an tsaro sun kuma kama wasu mutane goma sha daya da ake zargi da satar mutanen.

Yace an bibiyi mutanen da ake zargi masu yin garkuwa da mutanen ne, har aka kai ka gama su.

ASP Muhammad ya ce ana ci gaba da bincike, kuma nan gaba za su yi bayanin halin da mutanen su ke ciki, kuma ko an biya kudin fansa ko kuma ba a biya ba.