Jam'iyyar Musulinci ta yi nasara a zaben Morocco

Morocco

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Ma'aikatar cikin gida ta ce kashi 43 na masu zabe sun kada kuri'unsu

Jam'iyyar Musulinci ta Justice and Development Party (PJD) da ke mulkin Morocco ta lashe zaben majalisar dokokin kasar.

Jam'iyar ta cinye zaben kujeru 99 bayan an kirga kashi 90 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da jam'iyyar da ke hamayya da ita ta the Authenticity and Modernity Party ta lashe kujeru 80.

Jam'iyyar PJD ta ce yin ta-zarce a karo na biyu zai ba ta damar gudanar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki da walwalar jama'a.

Wannan ne karo na biyu da Morocco ke gudanar da zabe tun bayan da ta gyara kundin tsarin mulkinta a shekarar 2011.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Firai Minista Abdelilah Benkirane ya ji dadin zaben nasarar da PJD ta yi

Jam'iyyar Istiqlal ta samu ra'ayin rikau ta lashe kujeru 31.

Sauran jam'iyyun sun samu kujeru 305 da aka yi takararsu, yayin da aka bar wa mata kujeru 90.