An yi zanga-zanga kan auren jinsi daya a Australia

Australia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar na so majalisar dokokin kasar ta amince a rika auren jinsi daya.

Daruruwan masu goyon bayan auren jinsi daya Australia sun yi zanga-zanga domin bijirewa yunkurin gudanar da kuri'ar raba-gardama kan batun.

Gwamnatin kasar dai tana so a yi zaben raba-gardaman ne a watan Fabrairu kan ko a hana ko kuma a amince da aure jinsi daya.

Sai dai masu zanga-zangar -- wadanda suka mamaye titunan biranen Sydney da Melbourne -- suna so majalisar dokokin kasar ta amince a rika auren jinsi daya.

Australia na daya daga cikin kasashe masu arziki da suka haramta auren jinsi daya.