Mun sami miliyoyin kuɗaɗe a gidajen alkalai — DSS

Babban mai shari'a na Nigeria, Mahmud Mohammed
Bayanan hoto,

A kwanan nan hukumar kula da harkokin shari'a ta Nigeriya ta kori wasu alkalai kan laifin almundahana

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya wato DSS, ta ce, ta gano makudan kudade a gidajen wasu alkalai a jihohin kasar.

Hukumar ta ce ta gano kudaden ne a wani sumame da ta kai gidajen masu shari'ar da safiyar ranar Asabar.

Jami'an hukumar dai sun kaddamar da sumamen ne a babban birnin kasar, Abuja da Port Harcourt da Gombe da Kano da Enugu da kuma Sokoto.

A wani taron manema labarai da hukumar ta yi a Abuja, ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar ta DSS, Abdullahi Garba, ya ce jami'an sun samu kudaden kasashen waje da na gida, yayin sumamen.

Kuɗaɗen da aka samu a gidajen alkalai

  • N93,558,000.00
  • $530,087
  • £25,970
  • €5,680

Alkalan da aka kai wa samame sun hada da na Kotun koli da na Kotun Daukaka Kara da kuma na Manyan Kotunan kasar.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce an samu 'yar hatsaniya tsakanin jami'an hukumar da 'yan dabar da wani alkali bisa hadin gwiwar gwamnan jihar Rivers, suka yi hayar su.

Bayanan sirri kuma sun tabbatar wa hukumar cewa alkalin yana boye da kudin da suka kai Dala miliyan biyu, a cikin gidansa.

Sanarwar ta kara da cewa a dai-dai wannan lokaci kuma alkalin bisa goyon bayan gwamnan suka dauke makudan kudaden zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.

Sai dai kuma Hukumar ta DSS ta ce tana aiki tukuru wajen gano inda aka boye wadannan kudaden.

Baya ga wadancan kudade da DSS suka ce sun samu a gidajen alkalan, an kuma samu wasu takardun da suke dauke da bayanai kan mallakar manyan rukunan gidaje.

Yanzu haka dai hukumar ta ce tana kokarin gurfanar da alkalan ne a gaban kuliya.

Sai dai kuma wasu na yi wa hukumar ta DSS kallon wuce gona da iri.

Ana dai ganin cewa kai irin wannan samame a kan alkalai tamkar keta alfarmar bangaren Shari'ar kasar ne.

Karin Bayani

An dade dai ana zargin alkalan Najeriya da cin hanci.

Ko makonni kimanin biyu da suka gabata sai da Hukumar da ke sa ido kan harkokin shari'a a kasar ta kori wasu manyan alkalai bisa samun su da laifin cin hanci.

An dai kori babban alkakin kotun jihar Kano, mai shari'a Kabiru Auta da babban alkalin kotun daukaka kara da ke zama a Ilorin, mai shari'a Mohammed Ladan Tsamiya.

Da kuma babban alkalin kotun Enugu, mai shari'a I. A. Umezulike.

Hukumar ta ce ta kori wasu daga cikin alkalan bisa karbar na-goro game da batutuwan da suka shafi zaben kasar na shekarar 2015.

Tun dai hawan mulkin kasar, Muhammadu Buhari, ya lashi takobin yaki da rashawa da cin hanci da suka yi wa kasar dabaibayi.