Jordi Alba zai yi jinyar kwanaki goma

Spain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alba ya yi rauni ne a kafarsa a lokacin da yake buga wa tawagar Spaniya wasa

Barcelona ta ce mai tsaron bayanta, Jordi Alba, zai yi jinyar kwanaki goma.

Alba ya yi rauni ne a karawar da Italiya ta karbi bakuncin Spaniya a wasan shiga gasar kofin duniya da suka kara a ranar Alhamis.

An kuma sauya dan kwallon a minti na 22, inda Nacho ya shiga fili a madadinsa.

Alba ya buga wa Barcelona wasanni takwas a kakar bana, karawar da bai buga ba sun hada da wanda kungiyar ta yi da Sevilla da kuma Alaves a gasar La Liga.