IS ta yi asarar kashi daya cikin uku na yankunanta

IS

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

IS na shan matsin lamba daga dakarun Syria da Iraq

Wata sabuwar kididdiga ta nuna cewa kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci ta rasa ikon fiye da kashi daya cikin uku na yankunan da a baya ke karkashin ikonta.

Masu sharhi a kan tsaro da yaki na his sun ce IS ta yi asarar kashi 28 na yankunan da ke hannunta tun daga watan Janairu na shekarar 2015 lokacin da take kan ganiyarta.

Kididdigar ta nuna cewa a wata tara na farkon wannan shekarar, yankunan da IS ke rike da su sun koma fadin murabba'i 65,500 daga murabba'i 78,000 - wato kamar fadin kasar Sri Lanka kenan.

Sai dai asarar yankunan da IS ke yi ta ragu a wata ukun da suka gabata zuwa watan Oktoban da muke ciki.

An kori IS daga kan iyakar Turkiyya da kimamin kilomita 10, yayin da dakarun Iraqi suka kwace sansanin jiragen saman Qayyarah wanda ke da nisan kilomita 60 daga Mosul, inda 'yan kungiayr ke da matukar karfi.

Kazalika birnin Manbij da kewayensa na kasar Syria ya kubuce daga hannun IS. Birnin dai yana da mahadar da ke kan iyakar Turkiyya zuwa tsohuwar hedikwatar kungiyar da ke Raqqa.