Ana zaman makoki a Haiti bayan mutuwar mutum 900

Haiti

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana ci gaba da binne mutanen da suka mutu

'Yan kasar Haiti sun fara makokin kwana uku sakamakon barnar da mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da Matthew ta yi.

Akalla mutum 900 ne suka mutu sakamakon mahaukaciyar guguwar.

Gwamnatin kasar ta ce dubban gidaje sun rushe sannan akalla mutum 350,000 na matukar bukatar taimako.

Kazalika ana fargabar barkewar cutar amai da gudawa, yayin da mutane da dama suka rasa abinci saboda barnar da guguwar da ta yi wa gonakinsu.

Mahaukaciyar guguwar ta Matthew ta tsallaka ta kudu maso gabashin kasar zuwa Amurka, inda ta kashe akalla mutum goma.

Ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa, kana ta lalata wutar lantarki da rushe gidaje a Florida, Georgia da kuma Kudu da Arewacin Carolina.