An ƙaƙaba dokar ta-ɓaci a Habasha

Habasha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sun zargi gwamnati da nuna son kai

Mahukunta a kasar Habasha sun sanya dokar ta-ɓaci ta wata shida.

An ƙaƙaba dokar ne sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da manyan kabilun kasar -- Oromo da Amhara -- suka aka kwashe wata da watanni suna yi a kasar.

Sun yi zanga-zangar ne domin nuna fushinsu kan cin zalinsu da suka ce gwamnatin na yi a bangaren tattalin arziki da rabon mukaman siyasa.

Arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda a makon jiya a wani wajen bikin al'adun gargajiya ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 55.

Masu fafutikar kare hakkin dan adam sun yi zargin cewa an kashe daruruwan mutane kanana aka kulle dubbansu tun lokacin da aka fara gangamin kin jinin na gwamnati.