Kun san wacece za ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa?

Gasar ta mata zalla ce
Bayanan hoto,

Gasar ta mata zalla ce

Sashen Hausa na BBC ya fitar da jerin sunayen matan da za su fafata domin lashe gasar Hikayata.

Gasar, wacce ita ce gasar rubutun kagaggen labari ga mata zalla da BBC Hausa ya bullo da ita, wani yunkuri ne na bai wa mata damar nuna irin basirar da Allah ya hore musu wurin rubutu da kirkirar labari.

Yanzu haka dai mun mika sunayen jerin matan da muka tace ga alkalai domin su tantance mata uku da suka yi zarra.

A cikin watan nan ne dai za a sanar da wadanda suka lashe gasar, sannan daga bisani a ba su kyaututtuka a wajen wani biki da za a yi a Abuja, babban birnin Najeriya.

Matan da ke cikin jerin sunayen su ne:

  • Aisha M. Yusuf

2. A'isha Muhammad Sabitu (A'ishar Mobil)

3. A'isha Umar Ahmad

4. Amina Gambo

5. Amina Hassan Abdulsalam

6. Binta Zakari Bello

7. Fatima Magaji,

8. Hassana Abdullahi Hunkuyi

9. Khadijat A. Ibrahim Mauta

10. Mairo Muhammad Mudi

11. Maryam Ali Ali

12. Maryam Nuhu Turau

13. Nazira Abdullahi

14. Patima Adamu

15. Sa'adatu Usman Babba

16. Sadiya Abdullahi Tsoho Kudan

17. Safiyyah Ummu Abdoul da Rufaida Omar

18. Salma Mohammed Ishaq

19. Salma Usman Isma'il

20. Suwaiba Abdullahi