'Dokar rabon gado ta sabawa addinin musulinci'

Sultan of Sokoto

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu 'yan majalisar dattawan suma sun nuna suka kan kudurin dokar

Malaman addinin musulunci a Najeriya sun fara sukar kudirin dokar da ke da nufin samar da daidaito tsakanin maza da mata a kasar, ciki har da batun gado.

Jagoran mabiya darikar Tijjaniyya a Najeriya, Khalifah Sheikh Isyaka Rabiu, na daga cikin masu sukar kudurin dokar kuma ya ce kudurin ya sabawa addinin musulunci.

Ya shaida wa BBC cewa "Allah SWT ya yi bayani dalla-dalla a cikin Al-kur'ani mai girma, kan yadda rabon gado zai kasance tun daga kan 'ya'ya mata da maza, da iyaye da matan mamaci, da ma duk wadannan suke da hakki a cikin rabon."

Tuni dai kudurin dokar ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawan kasar.

Sheikh Isyaka Rabi'u ya kuma yi kira da kakkausar murya da ayi watsi da dokar, domin kaucewa fushin Ubangiji.

Yace wannan doka ba za ta samu karbuwa ga musulmin kasar ba, da ma duniya baki daya.