Ana aurar da mata 'yan kasa da shekara 15 a duk dakika 7

Kananan yara mata a sansanin 'yan gudun hijira

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rahotan ya ce kananan yara mata da ke sansanoni 'yan gudun hijira na da hadarin yin auren wuri

Wani sabon bincike da kungiyar Kare kananan Yara ta Save The Children International ta yi, ya ce, ana aurar da yarinya mai shekaru kasa da 15, a kowacce dakika bakwai.

Binciken ya nuna cewa ana tursasawa kananan yara wadanda shekarunsu ba su wuce 10 ba, wajen aurar maza wadanda suka girme musu da shekaru da yawa.

Kungiyar dai ta ce irin wannan ta'ada ta fi karfi a kasashe kamar Afghanistan,Yemen, Indiya da kuma somalia.

Save the Children ta ce auren wuri na iya haifar da matsaloli a kowanne bangare na rayuwar mace.

Rikici da talauci da kuma wasu rikece-rikicen da suka shafi rayuwar dan adam na daga cikin manya-manyan dalilan da ke sanya a yi wa kanana yara mata auren wuri.

Kungiyar ta ta kara da cewa aurar da yara mata da wuri na janyo musu rashin samun damar more kuruciyarsu da yin ilimi da kuma samun cigaba a rayuwa.

'Adadin zai karu'

Rahoton wanda aka yi wa take da Every Last Girl, an karkasa kasashe ne kan mataki-mataki a kan yadda mace ke shan wahala a matsayinta na 'ya mace a wurin ilimi, auran wuri da kuma daukar ciki kafin aure.

Sauran matakan su ne mace-macen mata yayin haihuwa da kuma irin da kuma karancin yawan matan da ke taka rawa a majalisu.

Kasashen chadi da Niger da Jamuhuriyyar Tsakiyar Afirka da Mali da kuma Somaliya ne suka kasance a matakin karshe.

Rahoton ya ce kananan yara mata, wadanda ke yankunan da ake rikici na iya fuskantar auren wuri.

Hukumar da ke Kula da Yara ta Majisar Dinkin Duniya, Unicef, ta yi kiyasin cewa yawan matan da ake aurarwa da kurciyarsu zai karu da daga miliyan 700 zuwa kusan miliyan 950, a shekarar 2030.

Rahoton na Save The Children dai ya zo ne a dai-dai lokacin Ranar Yara Mata ta Duniya.