Shafukan sada zumunta sun hana leken asiri

Shafukan zumuntar sun ce ba za su bari a keta doka ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shafukan zumuntar sun ce ba za su bari a keta doka ba

Shafukan Facebook da Twitter da Instagram sun toshe hanyoyin samun bayanansu ga wani kamfani da ke leken asiri bayan da aka zarge shi da sayar da bayanan ga hukumomin tsaron Amurka.

Bayanan dai ka iya bai wa hukumomin leken asirin damar sanya idanu kan masu fafutika da 'yan rajin kare hakki a shafukan na sada zumunta.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta Amurka mai suna the American Civil Liberties Union ce dai ta wallafa wani rahoto da ke cewa kamfanin da ke auna al'amuran da ke faruwa a shafukan zumunta na Geofeedia, wanda ke Amurka, ya bar 'yan sanda sun yi kutse cikin wani bayani da ya nuna yadda wasu ke yin zanga-zanga.

An wallafa wannan rahoto ne a daidai lokacin da ake nuna fargaba kan yadda shafukan sada zumunta ke dasawa da hukumomin gwamnati.

Geofeedia ya kare matakin da ya dauka, yana mai cewa yana kare lafiyar masu amfani da shi.

Ya ce ya dauki matakin baya bayan nan ne domin bai wa hukumomi damar tallafawa mutanen da mahaukaciyar guguwar Matthew ta shafa.