Bama-bamai sun kashe mutane da dama a Maiduguri

Ba a san yawan mutanen da suka mutu ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sha kai hare-hare a birnin Maiduguri

Hukumomi a Najeriya sun ce mutum takwas ne suka mutu sakamakon harin bama-bamai da aka kai a birnin Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya.

Jami'in hukumar bayar da agajin gaggawa a arewa maso gabashin kasar, Muhammad Kanal, ya shaida wa BBC cewa mutum 15 sun ji munanan raunuka kuma an kwantar da su a asibiti.

Ganau sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a tashar motar Muna da ke cikin birnin.

Wani da ya shaida lamarin ya ce "bama-baman sun tashi ne a daidai lokacin da muke shirin shiga motoci domin tafiya zuwa garin Gamborou, kuma mun kwashi gawarwakin mutum takwas."

Babu wanda ya dauki alhakin harin kawo yanzu, amma birnin na Maiduguri dai ya sha fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Sai dai an dade ba a samu rahotannin tashin bama-bamai a birnin ba, wanda nan ne cibiyar kungiyar ta Boko Haram.

Sojojin kasar dai na cewa sun ci lagon 'yan kungiyar ta Boko Haram sakamakon fatattakarsu da suke yi.

Amma shugaban wani bangare na kungiyar, Abubakar Shekau, wanda ya fito a wani sabon bidiyo kwanakin baya, ya ce har yanzu suna nan da karfinsu.

Kawo yanzu jami'an tsaro ba su ce komai game da lamarin ba.