Shi'a: An kashe mutum goma a Katsina

'Yan kungiyar 'yan Uwa Musulmi a Katsina

Asalin hoton, HRW

Bayanan hoto,

Mutane da dama sun samu raunuka a tarzoma

Rahotanni daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya na cewa an kashe akalla mutum goma lokacin da 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a suke taro.

Bayanan da BBC ta samu sun ce lamarin ya faru ne a garin Funtua lokacin da 'yan sanda da sojoji suka yi yunkurin hana 'yan Shi'a yin tattaki da suka saba yi duk shekara domin tunawa da ranar Ashura.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya kirga gawarwakin mutum takwas.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.

Ya kara da cewa an jibge jami'an tsaro a kusa da wurin da suke yin tattakin domin hana su, yana mai cewa jami'an tsaron sun rika harba bindiga sama domin tsorata jama'a.

Da ma dai jihohin Kaduna da Kano da kuma Katsina sun hana 'yan Shi'a yin tattaki a wannan shekarar.

Hasalima, jihar Kaduna ta haramta kungiyar saboda zarginta da keta dokoki da kuma tayar da zaune tsaye, zargin da suka musanta.

Halin da ake ciki a Kaduna:

Asalin hoton, Ali Kakaki

Bayanan hoto,

Mabiya Shi'a suna yin tattaki a jihohi daban-daban

A halin yanzu dai an tsaurara matakan tsaro a Kaduna a ranar da ake kyautata zaton yan kungiyar Islamic movement mabiya mazhabar shia za su yi muzaharar ranar Ashura.

Wakilin BBC da ke Kaduna ya ce 'yan sanda da sojojin jihar, har ma da tankokin yaki na sintiri a garuruwan da ke Kaduna da Zaria inda nan ne hedikwatar kungiyar.

Duk dai yan kungiyar ba su sami damar gudanar da zanga zanga ko muzahara kamar yadda suka saba ba,rahotanni na cewa an kona gidan shugaban kungiyar Malam Mutari Sahabi dake Unguwar Tudunwada da ke jihar Kaduna.

Bayanai na nuna cewa matasa yan unguwa ne suka kona gidan shugaban kungiyar ta yan Shia na dake jihar.

A yanzu dai matasa na ci gaba da wawashe kayan gidan da ba su kone ba.

An tabbatar cewa mutane biyu sun rasa rayukansu.

Asalin hoton, HRW

Bayanan hoto,

A Disambar 2015 ne aka kama shugaban 'yan Shi'a

Asalin hoton, HRW

Bayanan hoto,

A makon jiya ne gwamnatin jihar Kaduna ta haramta kungiyar ta 'yan shi'a.