An dage shari'ar matar da ta yi ridda a Pakistan

Malaman addinin Musulinci sun yi wa alkalan kotun barazana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Malaman addinin Musulinci sun yi wa alkalan kotun barazana

Kotun Kolin Pakistan ta dage shari'ar da take yi wa matar da ake zargi da yin ridda bayan daya daga cikin alkalan kotun ya janye daga karar saboda zargin saba ka'ida.

An jibge 'yan sandan kwamtar da tarzoma a wajen kotun da ke birnin Islamabad bayan wasu malaman addinin Musulinci sun yi wa alkalan kotun barazana.

Shekaru shida da suka gabata ne dai aka yanke wa Asia Bibi hukuncin kisan kai bayan an same ta da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) lokacin da suke yin jayayya tsakaninta da wata mace.

Alkalin da ya janye daga karar, Iqbal Hameed ur Rehman, ya ce ba zai yi hukunci a karar ba saboda ya yi alkalanci a kan wani dan siyasa, Salman Taseer, wanda aka kashe bayan ya yi magana da yawun Asia Bibi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce ana keta dokokin addini sau da dama a kasar domin huce haushi kan mutanen da basu ji ba basu gani ba.