Nigeria: An saki wasu 'yan matan Chibok '21'

A shekarar 2014 aka sace matan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sace 'yan matan Chibok ya ja hankalin duniya sosai

Wani babban jami'in gwamnatin Najeriya ya shaida wa BBC cewa an saki 'yan matan Chibok 21 daga cikin 217 da ke hannun kungiyar Boko Haram.

Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya tabbatar da labarin, inda ya ce 'yan matan na hannun jami'an tsaro a Maidiguri da ke jihar Borno.

Ya ce, "An sako matan ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da Boko Haram sakamakon shiga tsakanin da gwamnatin Switzeland da kungiyar International Red Cross suka yi."

Malam Garba ya ce za a ci gaba da tattaunawa da 'yan kungiyar ta Boko Haram domin sako sauran matan da ke hannu.

Ya kara da cewa a nan gaba kadan ne za a bayyana sunayen matan da aka saka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekarar 2014 aka sace matan

A baya an sha fitar da labarai marasa tushe kan sakin 'yan matan na Chibok.

Sakin matan Chibok 21 wata babbar nasara ce ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wacce take shan suka daga wajen masu fafutikar ganin an ceto 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan fiye da 250 daga makarantar sakandare ta Chibok a watan Afrilun 2014 - lamarin da ya ja hankalin duniya sosai.