China ta zarce Amurka a yawan biloniyoyi

Shugaban rukunin kamfanonin Alibaba Jack Ma shi ne na biyu

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban rukunin kamfanonin Alibaba Jack Ma shi ne na biyu

Wata kididdiga kan mutanen da suka fi kudi da China ta fitar ta nuna cewa kasar ta zarta Amurka sosai a yawan hamshakan masu kudi.

Fitaccen dan kasuwar gidaje nan Wang Jianlin ne kan gaba a jerin mutum 594 da suka fi kudi a kasar, yayin da Amurka ke da hamshakan masu kudi 535.

Shugaban rukunin kamfanin Alibaba, Jack Ma shi ne na biyu, inda dukiyarsa ta karu da kashi 41 daga shekarar da ta gabata.

Kamfanin wallafa bayanai na Shanghai mai suna Hurun ne ya fitar da jerin sunayen, kuma ana kwantan shi da mujallar the Forbes ta Amurka.

Sai dai babu daya daga cikin hamshakan masu kudin China da ke cikin manyan masu kudi 20 na duniya.

Wang Jianlin ya mallaki kudin da suka kai $32.1bn, yayin Jack Ma ke da $30.6bn, shi kuma Pony Ma mai shafin wasanni na intanet ke a matsayi na uku da $24.6bn.