Bob Dylan ya lashe kyautar Nobel kan Adabi

Asalin hoton, AFP
Wakokinsa sun shahara a shekarun 1960.
Mawakin nan dan Amurka Bob Dylan ya lashe lambar yabo ta Nobel a fannin adabi ta shekarar 2016.
Mawakin mai shekara 75 ya lashe kyautar ne saboda "ya kirkiri wani sabon salon waka a cikin tsarin wakokin Amurka".
An haifi Dylan a shekarar a shekarar 1941 da sunan Robert Allen Zimmerman kuma ya fara waka ne a shekarar 1959.
Wakokinsa sun shahara a shekarun 1960.
Wasu daga cikin fitattun wakokinsa su ne Blowin' in the Wind da The Times They are A-Changin', wadanda ke da maudu'in adawa da yaki da kuma tabbatar da 'yancin dan adam.