Aisha ta gargadi Muhammadu Buhari

Bayanan bidiyo,

Hirar BBC da Aisha Buhari na tayar da kura

Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta gargadi mijinta cewa ba za ta goyi bayan takararsa a 2019 ba idan har al'amura suka ci gaba da tafiya a haka.

A wata hira da ta musamman da BBC, ta ce gwamnatin mai gidanta ya yi watsi da fiye da rabin mutanen da suka yi mata wahala har ta samu mulki.

"Bai gaya min cewa zai tsaya ko ba zai tsaya ba tukunna, amma na yanke shawara a matsayina na matarsa, cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, to ba zan shiga cikin tafiyar ba.

"Idan har abubuwa ba su sauya ba, to ba zan fita na yi yakin neman zabe kamar yadda na yi a baya ba. Ba zan sake yi ba".

Sai dai shugaban ya ce aikin ta shi ne dafa abinci

Za ku iya sauraran hirar da ta yi wannan bayani da sauran muhimman abubuwan da ta fada a shirinmu na Ganemi Mini Hanya a ranar Asabar.

Ta ce shugaban bai san mafi yawan mutanen da ya nada a cikin gwamnatinsa ba.

Ta kara da cewa wasu "'yan tsiraru" ne suke juya akalar gwamnati, inda suke zabar mutanen da ake bai wa mukami.

'Kan 'yan APC ya rabu'

Bayanin da Mista Buhari ya yi a lokacin da aka rantsar da shi cewa, "babu wanda zai juya shi, kuma shi na kowa ne," ya ja hankalin mutane sosai.

Sai dai kalaman na matarsa, da ma wadanda wasu masu kusanci da gwamnatin ke fada, na nuni da cewa lamarin ba haka yake ba.

A cewarta, "Shugaban bai san mutane 45 daga cikin 50 (alal misali) da ya nada ba, kuma ni ma ban sansu ba duk da cewa na shafe shekaru 27 tare da shi".

Aisha Buhari ta roki wadanda ta ce suna hana ruwa gudu da su tausayawa jama'a su daina abin da suke yi, sai dai ba ta kama sunan kowa ba.

Ta kara da cewa ba ta jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin kasar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane da dama na zargin gwamnatin Shugaba Buhari da rashin sanin alkibla

A cewarta, "Mutane da yawa sun fara rarraba kawunan 'yan jam'iyyar APC, kuma hakan yana kawo mana damuwa da yawa yanzu. Saboda suna ganin su suka yi wahala amma ba sa koina yau".

Ta kara da cewa, "Wadanda ba su yi wahala ba; ba su da katin zabe su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi".

Bayanan sauti

'Yan Nigeria ka iya yi wa Buhari bore — Aisha Buhari

Wasu daga cikin tambayoyin da Naziru Mikailu ya yiwa Aisha Buhari:

  • Zargin karkatar da kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a Borno
  • Su wane ne mutanen da suka kewaye Shugaba Buhari?
  • Anya Shugaba Buhari ne ke jan ragamar gwamnatin kuwa?
  • Kin yarda da abin da mutane ke cewa wasu 'yan tsirarun mutane ne ke tafiyar da gwamnati?
  • Ko ya gaya mata cewa zai tsaya takara a zaben 2019
  • Idan zai tsaya za ta goyi bayansa?
  • Su wanene wadanda aka yi watsi da su a APC?
  • Ya za ki kwatanta rayuwarku kafin ku hau mulki da kuma yanzu?
  • Kamar sa'o'i nawa kike iya samu a rana tare da mai gidanki?
  • Shin kin shaida masa cewa akwai matsala a tafiyar nan?
  • Me za ta ce game korafin da ake yi cewa tana yawan tafiye-tafiye?
  • A ina take samun kudaden da take gudanar da ayyukan ofis dinta?