An gurfanar da 'yan Shi'a a kotun Kano

Ana zarginsu da hada baki wajen aikata laifi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zarginsu da hada baki wajen aikata laifi

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta gurfanar da wasu 'yan Shi'a a gaban kotu bisa zarginsu hada baki wajen aikata laifi.

Rundunar ta ce 'yan Shi'ar guda saba'in da bakwai na cikin wadanda suka yi tatattaki ranar Talata sabanin umarnin da gwamnati ta bayar cewa kada su yi.

Mutanen dai sun musanta aikata wani laifi, daga nan sai kotu ta dage zaman zuwa ranar 18 ga watan Nuwamba.

Tattakin da suka yi dai ya janyo takaddama tsakaninsu da mutanen gari, lamarin da ya sa suka.

Baya ga jihar ta Kano, an yi arangama tsakanin 'yan sanda da mabiya Shia'a da ma mutanen gari a jihohin Kaduna da Katsina a ranar ta Talata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Jihar Kaduna dai ta haramta kungiyar ta 'yan Shia baki daya, kuma tana neman kakakin kungiyar ruwa-a-jallo saboda zarginsa da keta doka.

A watan Disambar shekarar 2015 aka yi arangama tsakanin sojojin kasar da 'yan Shi'a a garin Zaria lamarin da ya kai ga jhalaka mutane da dama da kuma kama shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da wasu mabiyansa.