Iraki: IS ta kai hari da jirgi maras matuki

Asalin hoton, EPA
Mayakan Peshmerga na fafatawa da na kungiyar IS
Kungiyar IS da ke ikirarin jihadi ta kai wani mummunan hari a arewacin Iraki inda suka yi amfani da jirgin sama mara matuki da ke dauke da wani abu mai fashewa.
Jami'an Kur-dawa sun tabbatar cewa an kashe masu sojojinsu biyu, kuma an raunata sojojin Faransa biyu.
Wakilin BBC ya ce sojojin sun nufi wurin da jirgin saman mara matuki da ke dauke da bam ya fada kuma ya fashe lokacin da suke kokarin dubawa.
Mayakan kungiyar IS sun dade suna amfani da kananan jiragen sama da ake sarsafasu daga nesa domin tattara bayanan sirri.
Sai dai wannan shi ne karon farko da suka yi amfani da jirgin saman da ya janyo asarar rayuka.