Abubakar Adam zai karbi kyautar NLNG, Naira miliyan 40

Abubakar Adam Ibrahim
Bayanan hoto,

Abubakar Adam Ibrahim na cikin marubutan da ke tashe a Afirka

An bayyana littafin Abubakar Adam Ibrahim, Season of Crimson Blossoms, a matsayin wanda ya lashe Kyautar Adabi ta Najeriya ta NLNG ta 2016.

Littafin na cikin littattafai ukun da aka zaba don fitar da gwarzon adabi na bana a watan jiya.

Sauran littattafan da Season of Crimson Blossoms ya yi takara da su su ne Born on a Tuesday na Elnathan John, da Night Dancer na Chika Unigwe.

Da wannan nasara dai, Abubakar Adam Ibrahim zai karbi kyautar kudi dalar Amurka 100,000 (kwatankwacin miliyan 40 na naira).

Littafin na Season of Crimson Blossoms ya yi magana ne a kan wani nau'i na soyayya da ba kasafai ake ganin irinsa ba, musamman a arewacin Najeriya, inda wata baiwar Allah da ta manyanta ta ke soyayya da wani matashi da ya shiga gidanta da nufin sata.

Bayan rubuta littafin, da ma Born on a Tuesday, ma'abota harkar adabi a Afirka sun bayyana Abubakar Adam da Elnathan John a matsayin matasan marubuta da a yanzu haka ake ji-da-su a fagen adabi a nahiyar.

Burin Abubakar:

A wata hira da suka yi da Sashen Hausa na BBC a watannin baya, marubutan sun ce sun rungumi harkar rubuce-rubuce ne da nufin bayar da labarin Arewacin Najeriya, a maimakon su zuba ido suna kallo wadansu marubuta daga wadansu wurare na zayyana rayuwa a yankin yadda suka ga dama.

Marubucin dai dan jarida ne, kuma shi ne yake kula da shafukan adabi da fasaha a jaridar Daily Trust on Sunday.

Kamfanin gas na Najeriya, wato Nigeria Liquefied Natural Gas (NLNG) ne ya assasa kyautar, wacce duk shekara ake bai wa marubucin da ya yi fice a wani bangaren rubutun adabin Ingilishi a Najeriya, kama daga kagaggen labari zuwa rubutaccen wasan kwaikwayo da rubutattun wakoki zuwa littafai don yara kanana.

Kamfanin ya ce manufarsa ta bayar da kyautar ita ce karfafa gwiwar marubuta adabi a kasar.