Lauyoyi sun janye daga kare maharin Paris

Salah Abdulsalam, maharin da ake zargi.

Asalin hoton, BELGIAN/FRENCH POLICE

Bayanan hoto,

Salah Abdulsalam, wanda ake zargi da kai harin da ya kashe daruruwan mutane a birnin Paris a watan Nuwamban bara.

Lauyoyin da ke kare mutumin da ake zargi da kai hari a birnin Paris a watan Nuwamban da ya gabata, sun ce ba zasu cigaba da kare shi ba.

Frank Berton da Sven Mary sun fadawa wani gidan talibijin na Faransa cewa suna fatan mutumin da suke karewa Salah Abdulsalam zai bude baki ya yi magana.

Sai dai sun ce a akwai bayanai da ke cewa baya cikin hayacinsa kuma zai cigaba da amfani da hakkinsa na yin shiru.

Mista Berton ya ce mun sani kuma shi da kansa ya fada mana cewa ba zai yi magana ba kuma zai yi amfani da hakinsa na yin shiru da bakinsa.

A watan Maris daya gabata ne aka kama Salah Abdelsalam a kasar Belguim kuma yaki ya ce komai tun bayan da aka dawo da shi Faransa a watan Afrilun daya gabata.