Indonesia: An amince da hukuncin kashe mazakutan maza

Mata na zanga-zanga- kan cin zarafin mata a Indonesia
Bayanan hoto,

An samu afkuwar matsalolin lalata yara kanana da dama a Indnesia

Majalisar Dokoki a Indonesia ta kada kuriar da ta amince da yanke hukunci mai tsauri kan wasu sabbin dokoki, ciki har da amfani da wani sinadari wajen kashe mazakutar wadanda suka yi lalata da kananan yara.

Matakin ya biyo bayan watannin da aka shafe ana ta tafka mahawara mai zafi a Majalisar.

Wakiliyar BBC ta ce shugaba Joko Widodo, ya gabatar da sauye-sauyen ne bayan da jama'a suka nuna fushi kan fyaden da wasu maza suka yi wa wata yarinya mai shekara 14 a watan Mayun da ya gabata.

Sai dai wasu jam'iyyun adawa biyu sun nuna rashin amincewarsu kan dokokin, inda suka nuna damuwa game da yadda za a yi amfani da sinadarin da zai kashe mazakutar wadanda suka aikata laifin.