Amurka: An yi wa jagoran kamfen Hillary kutse

John Podesta da Hillary Clinton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

John Podesta na gaba-gaba cikin masu baiwa Hillary Clinton shawarwari.

Jagoran kamfen din 'yar takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton, John Podesta ya ce Hukumar tsaro ta FBI na gudanar da bincike game da ko Rasha ce ke da alhakin kutsen da aka yi masa a manhajar sakwanninsa na Email.

Mista Podesta ya kuma yi zargin cewa akwai yiwuwar dan takarar Republican ma Donald Trump na da masaniya game da lamarin.

Wadannan kalamai nasa na zuwa ne bayan da shafin kwarmata bayanai na WikiLeaks, ya wallafa wasu sakwannin nasa.

Babban mai bayar da shawara ga Misis Clinton din ya ce bincike na daya daga cikin wasu da dama da ake gudanarwa kan kutsen da wasu kungiyoyi da ke da alaka da Rasha ke yi wa jam'iyyar Democrats din.

Mista Podesta ya shaida wa manema labarai a yayin da yake shiga jirgin kamfen Hillary ce wa, "Na fa shekara biyar ana damawa dani a siyasa."

Jagoran da ya jima yana fafutukar yakin neman zaben Misis Hillary Clinton, ya ja hankalin al'umma ga wani rubutu da mai bai wa dan takarar Republican Donald Trump shawara, Roger Stone, ya yi a shafinsa na Twitter tun a watan Agosta, inda ya ce lokacin Mista Podesta na nan zuwa.

Amma kuma, jim kadan da fitowar wannan rubutu a shafin Mista Rogers na Twitter ne, shafin WikiLeaks ta kuma kwarmata sakwannin Mista Podestan.