Amurka da Rasha za su dinke barakar da ke tsakaninsu

Dubban Mutane sun mutu a rikicin Syria

Asalin hoton, MOD

Bayanan hoto,

Dubban Mutane sun mutu a rikicin Syria

Amurka da Rasha za su sake sabunta kokarinsu na kawo karshe rikicin da ake yi a Syria.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da takwaransa na Amurka John Kerry, za su gana a Switzerland a ranar asabar mai zuwa.

Mr Lavrov ya ce yana fatan za a tattaunawa mai muhimmanci a tsakaninsu.

A makon da ya gabata ne Amurka ta Rashan suka samu sabani akan yarjejeniyar d aka kulla saboda wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria.

'Yan tawayen da ke iko da gabashin birnin Aleppo na cigaba da kai hare-hare, a bangare guda kuma masu aikin ceto sun ce an kashe akalla