Zargin da ake mini a kan taba mata bita-da-kulli ne —Trump

Asalin hoton, Reuters
Trump ya yi watsi da zargin da ake masa
Ofishin yakin zaben Donald Trump ya mayar da martani cikin fushi game da wani zargi da wata jarida ke masa cewa ya taba jikin wasu mata biyu ba da son ransu ba.
Mai magana da yawun dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Republican ya yi watsi da abinda jaridar ta New York Times ta wallafa, Sannan ya zargi jaridar da tono abinda ya wuce shekara da shekaru inda ya ce yunkuri ne na bata wa Mr Trump suna.
Daya daga cikin matan ta zargi Mr Trump da ci mata zarafi ta hanyar tabata a cikin jirgi shekaru 30 da suka gabata, inda ta kamanta shi da