'Yan tsiraru sun mamaye gwamnatin Buhari — Aisha Buhari

Bayanan sauti

Hirar BBC ta musamman da Aisha Buhari

Mai dakin Shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijninta, Shugaba Muhammadu Buhari, inda suke hana ruwa gudu.

A wata kebantacciyar hira da ta yi da BBC, Misis Buhari, wacce ba ta bayyana sunayen mutanen ba, sai dai ta ce 'yan Nigeria sun sansu kuma tana tsoron boren da za su iya yi.

Aisha Buhari ta kara da cewa shugaba Buharin ya yi watsi da wasu 'ya'yan jam'iyyar APC wadanda suka sha wahala da mijin nata a lokacin gangamin yakin zabe.

Hajiya Aisha, ta ce lamarin ya sa ana samun rabuwar kawuna tsakanin 'yan jam'iyyar.

A cewarta, "Mutane da yawa sun fara rarraba kawunan 'yan jam'iyyar APC, kuma hakan yana kawo mana damuwa da yawa yanzu. Saboda suna ganin su suka yi wahala amma ba sa koina yau".

Ta kara da cewa, "Wadanda ba su yi wahala ba; wadanda ko katin zabe ba su da shi su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi".

An tambayi Misis Buhari ko mai gidanta ya san da wannan korafi, sai ta ce "ko ya sani ko bai sani ba wadanda suka zabe shi sun sani. Babu kuma abin da zan gaya masa don yana kallon abin da ke faruwa".

Uwargidan shugaban na Najeriya ta ce Shugaba Buhari bai san akasarin mutanen da ya nada a mulki ba, tana mai cewa yawancin mutanen da ke tare da shi 'yan-ta-yi-dadi ne.

"Cikin wadanda ya zaba ya nada idan an tambaye shi 45 cikin 50 ba saninsu ya yi ba. Bai san su ba. Haka nake zato. Ni ma ban san su ba saboda na zauna da shi shekara 27," a cewar ta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane da dama na zargin gwamnatin Shugaba Buhari da rashin sanin alkibla

Wannan wani bangare ne na hirar da muka yi da ita, inda a ranar Litinin ta yi magana kan irin aikace-aikacen da ofishinta ke gudanarwa domin tallafawa mata masu karafin karfi da kuma 'yan gudun hijira a Arewa maso Gabas.

Aisha Buhari ta ce mai gidan na ta bai gaya mata matsayinsa kan sake tsayawa takara a shekarar 2019, tana mai cewa "amma ni na yanke hukunci".

Sai ku kasance tare da mu a shirinmu na safe ranar Juma'a domin jin hukuncin da ta yanke da ma cikakkiyar hirarmu da ita.

Wasu daga cikin tambayoyin da Naziru Mikailu ya yiwa Aisha Buhari:

Bayanan hoto,

Aisha Buhari ta ce ya kamata a sauya yadda al'amura ke tafiya a gwamnatin Shugaba Buhari

  • Zargin karkatar da kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a Borno
  • Su wane ne mutanen da suka kewaye Shugaba Buhari?
  • Anya Shugaba Buhari ne ke jan ragamar gwamnatin kuwa?
  • Kin yarda da abin da mutane ke cewa wasu 'yan tsirarun mutane ne ke tafiyar da gwamnati?
  • Ko ya gaya mata cewa zai tsaya takara a zaben 2019
  • Idan zai tsaya za ta goyi bayansa?
  • Su wanene wadanda aka yi watsi da su a APC?
  • Ya za ki kwatanta rayuwarku kafin ku hau mulki da kuma yanzu?
  • Kamar sa'o'i nawa kike iya samu a rana tare da mai gidanki?
  • Shin kin shaida masa cewa akwai matsala a tafiyar nan?
  • Me za ta ce game korafin da ake yi cewa tana yawan tafiye-tafiye?
  • A ina take samun kudaden da take gudanar da ayyukan ofis dinta?

Kada ku manta za ku iya kallo da sauraren hirar a talabijin da shafunmu na intanet, bbchausa.com