Rikicin Kwankwaso da Ganduje na ci gaba da karuwa

Bayanan sauti

Kwankwaso da Ganduje sun dade suna tare a matsayin aminai

Rikicin dai ya barke tsakanin tsohon gwmanan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje na cigaba da karuwa.

Lamarin dai yayi kamari ne bayan da aka yi zargin cewar mataimakin shugaban jam'iyyar APC na arewa maso yammacin kasar, Inuwa Abdulkadir, ya ce korar tsoffin shugabannin jam'iyyar ta Kano ya dace.

Sai dai Inuwa Abdulkadir ya musanta wannan zargi inda ya ce ba shi da masaniya a kan batun.

A ranar Talata ne dai Kwamitin bincike kan rikicin jam'iyyar ta APC a Kano, karkashin jagorancin Sanata Muhammad Magoro, ya mika rahotonsa ga shugabancin jam'iyyar na yankin na arewa maso yammaci.

A 'yan watannin suka gabata ne aka hambare tsohon shugaban jam'iyyar APC ta jihar Kano, Umaru Doguwa, aka maye gurbinsa da Abdullahi Abbas.

Wakilinmu Mukhtar Bawa ta tattauna da bangarorin biyu, ku saurari yadda tattaunawar ta kasance.