Sarkin Thailand ya rasu yana da shekara 88

Sarki Bhumibol Adulyade

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan Thailand na matukar girmama sarki Bhumibol Adulyade

Sarkin Thailand, Bhumibol Adulyadej, wanda shi ne sarkin da ya fi kowanne dadewa a kan sarauta, ya mutu bayan ya kwashe shekara 70 a kan gadon sarauta.

'Yan kasar Thailand na matukar so tare da girmama Sarkin, mai shekara 88.

Ana ganin sa a matsayin wani mutum da ke fada-a-ji a kasar da ke fama da tashin-tashina da juyin mulki da dama.

A 'yan shekarun bayan nan ne ya sha fama da rashin lafiya lamarin da ya sa ba ya fitowa sosai cikin jama'a.

Mutuwar sarkin dai ta zo ne a lokacin da Thailand ke karkashin mulkin soja bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2014.

A ranar Lahadi ne dai masarautar ta yi gargadin cewar rashin lafiyar sarkin ta tsananta.