Ana cikin halin kaka na kayi a duniya - Guterres

Guterres ya ce babban kalubalensa shi ne kawo karshen rikicin Syria

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Guterres ya ce babban kalubalensa shi ne kawo karshen rikicin Syria

Sabon sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya yi gargadin cewa duniya yanzu na fuskantar wani mummunan yanayi.

A hirar sa ta farko tun bayan da aka zabe shi ba bu hamayya, ya shaidawa BBC cewa kawo karshen yakin da ake yi a Syria shi ne babban kalubale.

Ya ce duk wasu manya-manyan rikicin da ake yi a duniya na da alaka da Syria, dan haka ya kamata shugabannin kasashen duniya su fahimci cewa kawo karshen yakin na Syria zai amfani kowacce kasa.

Mr Guterres ya ce yana fatan irin hadin kan da aka bayar a majalisar dinkin duniya wajen zabarsa abinda ba a taba gani ba, alama ce cewa kasashen duniya za su mayar da hankali wajen magance irin matsalolin da duniya ke fuskanta.

Mr Gutteres wanda ya kasance babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, na shekaru goma, zai karbi mukamin Babban Sakataren Majalisar ne daga Ban Ki-Moon a watan Janairu.